Kwangilar kashe ku aka bamu daga kasashen waje inji sojoji

Daga Jaridar Al-Mizan

Mai karatu ga karshen hirar da Wakilinmu Abubakar Musa ya yi da Malama A’isha Yahaya wacce ta tsira da kyar a harin da sojoji suka kai Husainiyya a Disambar 2015. A bugu na 1223 a labarin ’yan gida daya wadanda suka tsira daga harin na sojoji, mun yi kuskuren cewa a Gyallesu ne, maimakon mu ce a Husainiyya a kanun labarin. A yi mana afuwa. Ba da gangan muka yi ba.

ALMIZAN: Kamar kwana nawa kuka yi a bariki kafin su sake ku?

A’ISHA YAHAYA: A bariki kwana daya muka yi, a wannan ranar da muka wuni a wannan ramin, to kuma ba ruwa ba ne (cikin ‘swimming pool’din kenan) inda suke yin fitsarinsu ne da bayan gidansu, don muna zaune, almajiran da suka kamo daga Gyallesu, duk wanda ya ce zai yi fitsari, sai su ce “ku yi masu, ai ba sallah su ke yi ba.” To, da son samu ne duk mun jujjuya, to sai suka shigo da burazu, sai suka tuttube suturar wasu burazun, sai suka ce kuma su zauna mu kallo su, su kallo mu, a haka, muka ki. To, saboda suna ta azabtar da wasu burazun fiye da mu, to shi ke nan sakamakon azabtar da su da suke yi, sai suka fuskance mu, amma ba wanda ya kalli kowa tsakani da Allah, kowa kawai ya yi kasa da kansa ne a cikin mu da su din. To, a haka ne kuma sai su shigo su ce waye wane, wane? Suna fadar fitattu a cikin mu. To, mu kuma inda Allah ya yi mana wata fikira, ko ga shi a cikin mu sai mu ce, “Ai kun kashe shi tun a can.” Ba mu yarda mun nuna masu wani a cikin mu ba, domin ba mu san abin da za su yi mana ba.

To, daga nan wajen La’asar sai suka fito da mu daga cikin ramin nan. Sai muka nemi ruwa za mu yi sallah, sai suka ce mana, “Da ma kuna sallah? To, ai ku ba Musulmi ba ne. Saboda an turo mu ne an ba mu kwangila a kanku. Akwai wasu mutane a Nijeriya, suna kiran kansu da Islamic Movement, amma su ba Musulmi ba ne, saboda haka meye bukatar za ku yi sallah? Ko a gabanmu ne za ku yi sallah?” Sai muka ce, “Lallai mu Musulmi ne, kuma tunda muna sallah, kuma a nan ma ba za mu fasa ba.” Sai wani ana ce masa Dan Zuru, dama shi ne ke ta yi mana isgili, har yana ce mana yana da ruwan zafi, yana da ‘tear gas.’ Yanzu ma wannan ramin zai cika mana shi ne da tafasasshen ruwa. Sai muka ce, “To, ai duk azaba, in ba ta Allah ba ce, ai za ta wuce. Yanzu duk azabar da za ka yi mana, muna mutuwa sai dai ka yi wa gangar jiki.” Sai ya ce, mu muna da taurin kai, randa muka rike makami kuma ya za a kasance? Sai muka ce, “Ba taurin kai ba ne gasikiya ce, da tsayuwa kyam a kan abin da muke yi, don mun san shi ne gaskiya.”

To, bayan sun hana mu ruwan alwala, sai suka ce mu yi taimama, in ji wannan Dan Zurun. Sai muka ce, “To ai in dai ga ruwa, taimama ba ta halasta ba, ba a yin taimama.” Sai wani ya ce, zai kawo mana fiya wota leda biyu. To, bayan mun yi alwalla mun mike mun fara kabbarar sallah, sai suka ce mu fasa sallar kowacce ta zauna. Sun ga fa mun fara sallar, sai aka ki zama, sai suka fara barazana da duka. Sun fara dukan ‘yan baya wasu kuma na cewa, “a dauko bindiga kawai a harbe su.” Lallai a lokacin tun da dai imani hawa-hawa ne, wasu sun zauna, amma wasu ba su zauna ba, sai da suka kai karshen sallarsu. Sannan kuma wadanda suka tsaya suka karasa sallar sun bar su sun karasa sallah a tsaye. Duka sun fara yi, amma sun ga ba a fasa sallar ba.

Bayan sallar, sai suka fara kiran mu dai-dai suna tambayar sunanka, shekarunka, ‘ya’yanka nawa da inda kake, suna dauka. Kuma daga nan duk da ba hijabai, sai suna daukar mu hotuna. Hall din yana da nisa, daga farkon hall din sai su sa ki a gaba, sun kuma sa mazan mu a gefe, ta gaban mazan za mu wuce saboda cin mutunci, kuma sun cire mana hijabai. Za ki wuce, ki bi tsawon hall din nan suna kallon tafiyarki. In ma sun ga kina da jiki za su doke ki, su ce dole sai kin yi gudu. To, a haka har karshe zuwa inda za su dauke ki hoto. Suna cewa za su nuna wa duniya ga shi sun cire mana hijabai, zai tabbatar da cewa mu ba Musulmi ba ne da sauransu. Ga shi sun hada mu maza da mata, dama abu kaza muke yi. To, mu hadu mu yi ta yin abu kazan. Suna fada mana kalmar da ake fada mana – ‘yan mutu’a, ‘yan mutu’a.

To, kuma wadannan suna ce mana dama Malam yana yin kasuwanci da mu ne, ai ko ma cikin mu saida aka zabo masu kyau, sannan ai abin da yake hada mu ke nan. Sannan a cikin Husainiyya akwai kudi, sannan yana nuna yawan mu a kyamarori ana turo masa da kudi daga kasashen waje. Yanzu mu a cikin mu ina ‘yar Malam? Sai aka yi shiru. Sai wani ya ce, “Sir ai ba ‘yar Malam a nan, duk suna gida suna sheke ayarsu.” Sai ya ce, ” To ina matar Malam?” Sai ya ce, “Sir kada ka bata lokacinka, ai nan duk matansa ne. Duk wadda yake so nan matarsa ce.” Sai muka ce, “Innalillahi wa innailaihi raji’un! Malam ya tsarkaka daga barin wannan wallahi!” To, a nan ne suka sa wani abu suka dudduke mu, saboda mun ce Malam ya tsarkaka daga barin haka.

To, haka dai muka samu kanmu har wajen Magariba, sannan suka yi waya, suka sa aka daho abinci, sai suka ce a zo a bi layi a karbi abinci, sai muka ki bin layin. Sai suka sa mana kowanne a gabansa, shinkafa ‘take-away’ da fiyawota daya. Ba wanda ya ce komai, sai kuma suka ce, “Inda mu ne ku, ba za mu ci abincin nan ba saboda kuna ce mana dawagitai, ya za a yi dawagitai su dafa abinci su ba ku ku ci? Jiya kuna gidanku kuna ce mana abin da kuka ga dama, kuna Labbaika ya Hussain, Labbaika ya Mahadi, yanzu ku kira su mana a nan. Yanzu kuna wajenmu, sai yadda muka yi da ku. Yanzu muka ga dama, kowa zai zabi matarsa a cikinku.” Sai mu muka ce, “Wallahi sai dai in ba ranmu, in dai muna da rai haka ba za ta taba kasancewa ba.”

Sai muka kara tattaro yaranmu mata a jikinmu, ko za a raba mana wajen kwanciya ba za a raba mu da su ba. To, ai a wannan lokacin sai suka ce bari su cire kananan yara masu kananan shekaru, su cire mata masu goyo, su cire mu marasa goyo kuma marasa kananan shekaru. Sai suka raba kashi uku. To, mu kuma wannan gorin abincin da suka yi mana, sai muka ce ba za mu ci abincin ba. Jiya ba mu ci ba, don yau ba mu ci ba, ai ba za mu mutu ba. Shi ke nan sai muka ki cin abincin, sai suka ce, “Ba za ku ci abincin ba ne?” Sai muka ce, ” Mun koshi. ” Sai muka yi banza da su.

To, can dai muna zaune, domin ba barci ake yi ba. Bayan sun cire yaran daban, masu goyo, mu kuma daban. To da kashin masu goyo da wadannan yaran nan suka bar su, mu kuma can wajen karfe biyun dare domin dai sun kwace waya kuma ba agogo, irin gari ya yi shiru din nan ne, sai suka zo da mota, ita ma kamar motar icce ce, amma ta karfe, sai suka ce a yi layi wannan kashin namu banda yara banda masu goyo, aka yi layi, to sai an yi layi an fara shiga, sai su koro mu baya, sun yi haka har sau uku, a na ukun ne sannan muka je.

Motar nan ko barkono suka zuba ko miye oho, suka dinga jefa mu a motar nan. To, akwai wata a Dogarawa take, tana da ciki, da suka jefa ta suka taka ta, sai ta ce, “Kai don Allah, ina fa da ciki!” Sai ya ce mata, “Wata nawa?” Sai ta ce,” Wata tara.” Sai ya ce, “Ai yanzu ma zan kashe abin da ke cikin.” Sai ya sa takalmi ya taka gefen cikin, to shi ne tun daga nan dai na ga alamar ba ta da lafiya. To, shi ke nan bayan sun gama sa mu, amma su ba dayan su da ya shiga motar. Sai suka kawo wannan barkonon, sai nan bakin motar suka yi layi da mu, amma ya kasance fuskarsu na kallon waje. Ka ga za su sha iska, duk kuma sun toshe mu, sai kuma aka kawo tamfol aka rufe mu. Ga shi mun matsu tun muna yin tari har ma ba wanda ke iya yin tarin, kuma da wadannan matan da na ce maka mu marasa goyo da wadannan ‘yan matan suka hada mu da burazu suka hada sun cika motar taf ba wajen numfashi.

To, Kaduna za su kai mu, amma ba su nufi Kaduna din ‘direct’ ba, sai suka yi ta yin yanke da mu ta daji-daji. In suka je tsakiyar daji sai su tsaya da mu, sai su sauka, sai kuma mu ga sun dau hanya inda ba za mu gan su ba, magana suke yi, me suke yi Allahu a’alamu, sai su kuma dawowa, sai su tafi da mu, sai da muka tsaya sau uku cikin daren nan. Sannan da suka isa Kaduna da mu, sai suka kai mu wani wajen ‘yan’uwansu. Da suka kai mu can sai suka fito da mu, sai suka ce ga shi a ajiye mu kafin safe. Sai Shugaban wajen ya ce, “Ina! Ai ajiye wadannan hadari ne, ai da daddaren nan za su kashe kowa su gudu.” Ya ki amsarmu, aka mai da mu mota, suka daure mu da wannan hijabin namu. Kamar yadda ake yi wa bayi din nan, haka aka yi mana.

Suka je suka nemi wani waje na biyu, suka je suka tattauna sannan aka ce a shigo da mu, nan ma aka sassauke mu. To, nan ma sai suka ce, ina! Ai amsar mu hadarine, aka ki amsar mu, aka dawo da mu aka kara shigar da mu mota, duk fa a cikin wannan dare na ranar Lahadi ke nan. To a guri na uku ne suka karbe mu, amma nan ma mu kadai aka amsa matan aure.

ALMIZAN: Wuraren da suke ajiye ku din, sojoji ne ko ‘yan sanda, ko kuwa dai ba ku gane ko wane wajene ba?

A’ISHA YAHAYA: Wajajen da suka fara kaimu na farko ‘yan sanda ne, na biyu sojoji ne, na uku inda aka karbe mu ‘Operation’ Yaki ne, inda muka zauna.

ALMIZAN: To, inda aka kai ku aka karbe ku, kamar kwana nawa kuka yi a nan?

A’ISHA YAHAYA: Inda aka karbe mu kwananmu shida. To, a nan kuma sai suka ce lallai sai dai su amshi wadannan matan kawai, amma su ma a na ukun cewa suka yi idan suka karbi mata da mazan nan duka waje daya, to ba su san aika-aikar da za mu yi cikin dare ba, duk mu kashe jami’an tsaro mu fasa mu gudu, mu shiga cikin gari mu rarraba. Sai suka amshi matan kawai su kuwa su Malam Iliya, su baban Yusuf, to daga nan ba mu san yadda aka yi da su ba, sai daga baya da muka dawo gida, sannan muka san ga yadda aka yi da su.

ALMIZAN: To, daga inda suka karbe ku, ina suka juye ku suka ce kowa ya tafi gida?

A’ISHA YAHAYA: To daga inda suka karbe mu, to daga nan ma sai muka sami wata ‘yar matsala, ka san na gaya maka ba mu ci abinci ba, nan ma daren saboda abin da suka yi mana ba mu ci abinci ba. Ka ga kwana biyu ke nan a haka. To, sai a daren suka fara yi mana tambayoyi, suka dai dan amshi abubuwan wajenmu. Na gaya maka a can da suka amshi ‘yan kunnaye mu biyu ba a ba mu namu ba. To, nan ma sun kara kwacewa, da ‘yan kunne da zobe da sarka duk suka kwace a cikin daren, nan ma ba mu yi bacci ba, domin an kawo mu ke nan aka fara kiran sallar Asuba. Shi ke nan sai da safe aka kawo mana abinci, aka kawo mana koko bai wuce rabin kofi-kofi ba. To, a nan ne na san mun amsa mun kakkarya. To, daga nan ne sai aka tambayi kowa shekarunsa. To a nan ma kusan kullum in ba a fito da mu ba a fito da mu sau uku sau hudu a dauki hotunanmu, sai a ce a fito da mu a dauki hotuna, kuma a nan ma sau daya ake ba mu abinci. In mun tashi da safe muka yi sallah, mukan zauna muna addu’o’i. To, akwai ma abin da sukayi mana su ‘yan wurin, su ‘Operation’ Yaki, wannan hada muryoyin da muke yi in muna addu’a, sai su zo su yi ta rawa. Karshe wajen kwana hudu sai suka nemi su hana mu yin addu’a a gurin. Wannan abin da muke yi sun fuskanci zai ja masu wani abu a gurin. To, da yake a gurin akwai wata yarinya kakarta ‘yar sanda ce mace, tana aiki a inda aka fara kai mu na biyu. To ita ce ta kara kawowa yarinyar koko, amma mu da aka kara kawo mana abinci sai karfe uku.

To, a ranar da aka kai mu dakin da aka kaimu bai wuce a ce karancinsa mutum 2 ko 3 ba, amma mu mutum 52 kuma dakin kamar sa ne guda biyu. Ya kasance ba dare ba rana duk a zaune muke, ba inda mutum zai kwanta. To, kasantuwar na ce maka akwai masu juna-biyu kusan mutum takwas, ‘yan’uwanmu in dare ya yi da yake an san mai ciki akwai son barci, sai sauran su firfito wajen bayi, su tsattsaya, duk a wajen ba ‘space’ in ba an sa darduma ba ne. Sai a ce mutum hudu masu ciki su kwanta su yi barci ko na awa daya. In sun tashi sai a ce su ma hudun su kwanta su yi barci. To a irin wannan barcin ne, da yake akwai wata mai harbi a cikin mu, wadda ba su kai ta asibiti ba, sun ki ba mu damar mu kai ta asibiti kuma duk kudin hannayenmu sun amshe suna hannunsu. Ita mai harbin a kafa sai take kuka. Ita mai harbin a cikin wannan dakin sai aka ajiye ta a nan benci inda su ‘Operation’ Yakin suke zaune da masu aikin kwana, ka san ba su barin wajen, sai na ga alamar harbin yana damun ta, tunda abin yana ruwa, kafar ta kumbura, sai na fito daga dakin na zo wajenta, sai take ce min, “Maman Mahadi rasuwa zan yi, ki kama ni ki kai ni bayi. ” Sai na kama ta na kai ta bayi. Sai muke magana cewa tunda muna da yawa, kuma ba mu san inda mazanmu da ‘yan’uwanmu suke ba, ya kamata a san fa ga inda muke, ga halin da muke ciki.

To kuma cikin mu ba mai waya. To Shugaban wajen sunansa Ali, shi ba ya aikin kwana ya tafi gida. To, da safe da ya zo sai na je wajen sa na yi sallama ofishinsa, sai na ce, “Ali.” Ya ce, “Na’am.” Na ce, “Ina so ka ba ni aron wayarka”. Sai ya ce, “Wayata kuma!” Sai na ce, “Eh.” Sai ya ce, “Me za ki yi da wayata?” Sai na ce, “Zan kira mijina in ji yana nan da rai ko kuwa kun kashe shi!” Sai ya ce, “Ai ba mu muka kashe shi ba, mu muka harbe ku a Husainiyya?” Sai na ce, “Ba ku ba ne, amma duk irin aikinku ne, ko kai aka kai za ka yi.” Sai ya ce, “Zan ara maki wayar. ” Sai ya ba ni wayar, ‘touch screen’ ce, sai na ce, “Ai ban iya amfani da wannan ba. ” Sai ya ce, “To, yanzu ya za ki yi?” Sai kuma ya ce, “Yanzu kina da lambar mijinki?” Sai na ce, “Ina da lambar mijina.” Sai ya ce, “Yanzu kuna nufin duk abin da aka yi maku ba ki mance komai ba?” Sai na ce, “Ni ba abin da na manta daga abin da kuka yi mana.” Sai ya ce, “Kin rike lambar?” Sai na ce, “Eh, na rike lambar”.

Shi ke nan ina fadi yana rubutawa, ya kira, sai kiran ya yanke, ya sake kira sai ba a dauka ba. Sai na ce, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Sai ya ce, “Sun kashe shi ne?” Sai na ce, “A’a ban sani ba. ” Sai na kara ‘trying’, sai na biyun sai ya dauka, sai ya ce, “Kuna nan da rai?” Sai na ce, “Eh muna nan da rai. ” Sai ya ce, ” Mu nawa ne?” Sai na fara fadi masa fitattu, sai na ce, “Amma ba zan iya fada maka ba ta waya, amma akwai Fatima Magume, Kwamandiya, Amma A’isha Danladi, Zainab Kiyaye ka.” Na ce, “Duka mu dai 51 ne mata.” Sai ya ce min, “To ina kika sami waya?” Sai na ce, “Ikon Allah,” shi dai yana tsaye yana jin mu. Sai ya ce in ba shi. Sai ya ce, “Ki ci gaba da wayarki, amma ba inda za ki matsa daga nan. ” Wato ba ya so in fadi wata magana wadda bai ji ba. Ina tsaye muka gama waya da babansu. To, a nan ne a ranar kowa ya san ga inda muke, tunda hatta wadannan yaran da aka raba mu da su masu goyo, ba wanda ya san inda aka kai su, mu ma ba mu san inda za a yi da mu ba. To, shi ne babansu ya fada wa mutane ga inda nake.

To, shi ne bayan dare ya yi ina kwance a dakin, sai ga shi Shugaban ya zo da kansa, ya yi sallama aka amsa. Ya ce, “Ina A’isha Yahaya?” Sai na ce, “Ga ni.” Sai ya ce, “Ga Maigidanki ya yi kira.” Sai na ce, “To.” Sai na taso na tsaya kusa da shi ina wayar, sai ya ce, “A’a ba damuwa, ki je duk inda kike so ki yi waya, inda ba wanda zai ji ku.” Sai na shiga ofis dinsa sai shi ya fito. Muna ta magana da babansu kusan awa daya, sai da ya ce, to ki ba mai wayar, sai na ce, “To”.

To, kullum in bai kira ni sau biyu ba, zai kira ni sau daya. To, a nan ne ma suka sami dama, ni kuma da ya ce, duk inda nake so in yi waya, sai in dawo da wayar cikin daki wajen ‘yan’uwa inda nake, saboda wasu suna so su yi waya, amma ga ba su da hanya, in zo in ba wannan sai ta kira ta yi magana. In ba wannan sai ta kira ta yi magana. A nan ne ma har Fatima Magume suka fadi ga inda makullin motarsu yake a je a dauka a fitar masu da motarsu. A nan ne aka fitar masu da motarsu.

Muna nan sai ran nan suka ce za a turo wani, ba mu san ko waye ba. To, ina ga mijin Fatima Zuru ne. Gaskiya dai don wahala mun sha, amma kamar yadda wasu ke fada, ko cin zarafi, ko fyade, gaskiya wannan ba wanda ya faru da mu. Allah bai ba su iko a kan haka ba gasikiya. Amma dai wahala da taka mutum a jiki da duka da bulala da bindiga, duk sun yi mana.

ALMIZAN: Da suka kwaso ku a mota ina suka kai ku?

A’ISHA YAHAYA: Kamar yadda na ce maka, mijin Fatima Zuru ne ya zo, tabbas mota uku aka yi da mu. To, da aka dauke mu sai aka kaimu inda aka sai mana abin da za mu karya. Shi mijin Fatima Zuru kenan. To, daga nan fa shi ne motocin bus-bus haka na haya aka dauke mu aka kai mu cikin Maraba, a Dogarawa. Sai burazu suka zo suka tare mu, aka raba mu gidaje kamar mutum goma-goma, a gidajen matansu a nan aka sa mana ruwa muka yi wanka, muka wanke kayan jikinmu, ko takalma babu, aka sai mana takalma, muka ci abincin rana. To daga nan ne su kuma burazun garin su ma suka kawo wata mota mai girma, to sai aka kwaso mu duka aka kawo mu nan cikin garin Zariya. To, daga nan su kuma su babansu suka zo da mota daga Hayin Ojo, aka dauke mu aka kai ‘yan Samaru gida, ‘yan Kwangila; mu dai ‘yan Hayin Ojo mune karshen kaiwa gida.

ALMIZAN: Wane kira kike da shi ga ‘yan’uwa?

A’ISHA YAHAYA: Kiran da nake da shi ga ‘yan’uwa, gaskiya tabbas in muna cikin barci, da gafala, da rafkana, to mu farka. Saboda ga shi suna cewa kwangila aka ba su, daga ina, sun fada mana da bakinsu, ai ba su sha za mu fito ba ne bare mu bayyana wannan sirrin. Sun fada. Amma ‘yan’uwa kamar mun shagala da kanmu ne. Mun shagala da wadanda suke son ganin bayanmu da addu’o’i da komai, amma kamar ‘yan’uwanka kake son gani a wani hali, ko ka ce me ya samu wadannan, sai ka kara fantsama abin. Ya kamata mu farka.

ALMIZAN: To wane kira kike da shi ga gwamnati?

A’ISHA YAHAYA: Kiran da nake da shi ga gwamnati shi ne, lallai su gaggauta sakar mana Maulanmu Shaikh Ibraheem Zakzaky, saboda sun kama shi sun tsare ba tare da hakki ba, da sauran ‘yan’uwanmu da suke a tsare.

ALMIZAN: To, mun gode.

One thought on “Kwangilar kashe ku aka bamu daga kasashen waje inji sojoji

  • December 28, 2019 at 3:12 am
    Permalink

    Allah sakamana a kawukansu mazansu da matansu yaransu da manyansu Albarkan mafificin halita amen.

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *