Janar Qassem Sulaimani Katanga ne ga yankinmu gaba daya -Qatar

Nasir Isa Ali.

Ministan Harkokin kasashen waje na Daular Qatar,Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani, ya ziyarci Tehran domin Isar da jajen sarkin Qatar da al’umarsu ga Tehran.

Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani Ya bayyana wa shugaba Rouhani cewar,kashe Janar Qassem Sulaimani ya kara mana fahimta game da muhimmancin aikin da yake gabatarwa, da kuma ya yadda ya zama katanga ga yankin namu baki daya. Kuma kisan ya nuna yadda ya tsaya gaban muradun makiya.
Ya kuma yaba da matakan hankalin da Iran take dauka wajen bibiyar wannan hakkin na Janar Qassem Sulaimani.
A nasa bangaren,shugaba Hassan Rouhani ya bayyana cewar, tunda sun san wanda yayi kisan,kuma akansu za’a rama.
Yayi godiya ga sarkin Qatar da mutanenta bisa wannan goyon baya da suka nuna wa Iran a irin wannan lokacin.

Shima shugaban Turkiyya Racip Tayyib Erdogan, ya buga wa shugaba Rouhani waya Indi yake taya shi da al’ua Iran da Iraqi jaje da kuma alhinin wannan rashin na wannan babban gwarzon.
Ya shedawa shugaban cewar,shima tare da ministansa na harkokin waje suna nan tafe domin yin jaje da ta’aziyya ga mutanen Iran.
Ya roki Iran da ta kara cigaba wajen yin amfani da hankali,hangen nesa kan wannan lamarin mai bakanta rai kamar yadda ta saba a duk lokacin da irin wannan din ya sameta.

Shugaba Assad na kasar Syria,ya aike da wata tawaga zuwa Tehran domin yiwa Iraniyawa jaje tare da nuna goyon bayan Syria da al’ummarta ga Iran.
Shugaba Assad ya bayyana cewar “Janar Sulaimani shine gwarzo kuma jarumin wannan karnin namu. Yace mutanen Syria zasu rubuta tarihi ga na baya cewar,Janar Qassem ya taimaka wa Siriyawa wajen ceto kasarsu daga yan ta’adda.
Yace,kashe Sulaimani a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Baghdad ya nuna wa duniya cewar,bisa izinin gwamnatin Iraqi ya ziyarci kasar,kuma bisa izininta zai bar kasar,don haka wannan sheda ce babba ga Iran da Iraqi. Yayin da su kuma yan ta’adda suka keto kasar ta barauniyar hanya suka kashe shi,kana suka sake tserewa ta barauniyar hanya. Yace yayin da aka gama da Amurka a cikin rigar ISIS,sai ta fito cikin rigar soja tayi ta’addamcinta.
Yayi Allah wadarai da Amurka da yan kanzaginta,sannan yace Iran tanada duk wani yancin yin ramuwa kan maksa Janar Sulaimani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *