Daga Haramin Sayyida Ma’asumah[SA] Sayyida Suhaila ta karbi kyautar karramawa a madadin Shaik Zakzkay[h]….

Sayyida Suhaila Kenan tana karbar kyautar girmamawa a madadin Jagora

A jiya Alhamis 26 ga watan Disamba 2019 aka gabatar da wani taro na musamman na tunawa da cikar shekaru 4 da mummunar waki’ar Zariya, a Haramin Sayyidah Fatimah Ma’asumah[SA] dake cikin birnin Qum na Iran.

A lokacin wannan babban taro wanda ya hada mahalarta daga ciki da wajen Iran, an karrama jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sayyid Ibrahim Zakzaky da kyauta ta musamman wanda ‘yar sa Sayyida Suhaila Ibrahim Zakzaky ta karba a madadin sa.

In ba’a manta ba yanzun an cika shekaru hudu cur da mummunar waki’ar Zariya wadda tayi sanadin shahadar sama da almajiran Malam 1000 da ciki harda ‘ya’yan sa uku.

Haka nan kuma tun a lokacin Malam [H] yake tsare a hannun gwamnatin Nigeria tare da hali na rashin lafiya da yake da shi tare da mai dakin sa Malama Zeenah.

Yau ake cika kwanaki 21 da mayar da Malam gidan kaso na Kaduna kuma har zuwa yau din ba’a bada dama ga likitocin sa su duba shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *